Sharuɗɗan sa’ayi tsakanin Safah da Marwah, Mahzuratul ihram (abinda harama ke hanawa)

Sharuɗɗan sa’ayi tsakanin Safah da Marwah
1- Yin niyyah.
2- Ya tabbatar ya yi zagaye bakwai cikakku.
3- Fara sa’ayin daga dutsen Safah.

Mahzuratul ihram (abinda harama ke hanawa)
1- Akwai wanda kaffararsa ita ce bayar da kwatankwacinsa, shine farauta.
2- Akwai wanda babu kaffara akansa, shine ɗaura aure.
3- Akwai wanda kaffararsa take da tsanani, shine yin jima’i.
4- Akwai wanda kaffararsa ita ce irin kaffarar laifin aske gashi, sune sanya ɗinkakkun kaya, shafa turare, aske gashi da yanke farce, Namiji ya rufe kansa da abinda yake manne da kansa, fitar da maniyyi ta hanyar shafar Mace, matuƙar bai kai ga saduwa ba

Manufar hajji mafi girma itace, Tauhidi don haka wajibi ne akanmu mu riƙa jin wannan al’amari mai girma, kuma tambarin Mahajjata a koyaushe yana ƙunshe da tauhidin Allah, kamar yadda hakan ya zo a cikin kalmomin talbiyyah (LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIK, LABBAIKAL LA SHARIKA LAKA LABBAIK, INNAL HAMDA WANNI’IMATA LAKA WAL MULKA, LA SHARIKA LAKA).

Check Also

Wajiban Hajj

1- Yin harama daga miƙati. 2- Tsayuwa a Arafah har zuwa dare. 3- Kwana a …